An samu mutum 119 da suka kamu da korona ranar Litinin a Najeriya
0
10/27/2020 03:52:00 AM
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 62,111 bayan da aka gano ƙarin mutum 119 da suka kamu da cutar ranar Litinin.
Adadin wadanda su ka rasa rayukansu sanadin cutar kawo yanzu ya kai mutun 1,132, yayin da a ka sallami mutun 57,571.
A jihar Legas an samu karin mutum 119 da suka kamu da cutar, sai FCT mai mutum 26.
Sai jihar Filato mai mutun 9, sai Edo mai mutun 4.
Jihar Oyo mai 2, inda a karshe jihar Nasarawa ke da mutun 1 tal.
Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.
Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
Tags