Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Dalibai A Hatsarin Mota
0
10/30/2020 07:14:00 AM
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kadu da hatsarin motar da ta salwantar da rayukan mutane da dama wanda yawancinsu yara ‘yan makaranta ne.
Buhari a sakon ta’aziyar da kakakinsa Femi Adesina, ya fitar a ranar Juma’a, ya aike ga iyayen yaran da suka rasu da al’ummar Karamar Hukumar Awgu da ke jihar Enugu, bisa mummanan hadarin.
Shugaba Buhari ya kuma mika sakon gaisuwarsa ga hukumar gudunarwar makarantar daliban tare da fatan za su samu rahamar ubangiji.
Daga karshe ya ja hankalin masu tuka ababawan hawa da suke tabbatar da lafiyar ababen hawansu, tare da guje wa tukin ganganci domin kauce wa salwantar dukiya da rayuka.