Sojoji da 'yan sanda a jihar Cross River na binciken wadanda suka kwashi ganimar gwamnati
Za a iya cewa zanga-zangar EndSars da matasa suka kwashe kimanin mako biybiyuu suna gudanarwa kan zargin cin zalin jama'a da rundunar 'yan sanda ta SARS ke yi, ta zamo irinta ta farko da ta girgiza kasar a shekaru 60 na kasancewar Najeriya kasa mai 'yancin cin gashin kai.
A ranar 8 ga Oktoban 2020 ne dai zanga-zangar ta fara kamari musamman a birnin tarayya Abuja da Legas kafin ministan Abuja ya kafa dokar hana zanga-zanga a birnin, abin da ya sa masu zanga-zangar suka koma rufe titunan manyan birnin, al'marin da kuma ya janyo cunkoson ababen hawa.
Sai dai duk da cewa sifeto janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammaed Adamu ya sanar da rushe rundunar ta SARS masu zanga-zangar sun ci gaba, inda kuma aka samu wani bangare da ke goyon bayan rundunar SARS ya fara dauki ba dadi da masu son a rushe rundunar.
Wannan al'amari ne dai ya janyo rikici har ya fantsama kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba musamman 'yan kasuwa kuma daga bisani wasu matasa a fadin kasar suka rinka farfasa rumbunan ajiyar abinci na gwamnati da ma gidajen 'yan siyasa domin kwasar ganima.
Darussa daga zanga-zangar EndSars
BBC ta tattauna da masana guda biyu a fannin tsaro da kimiyyar siyasa wato Malam Kabiru Adamu da Malam Kabiru Sufi kan darussan da ya kamata Najeriya ta koya daga makwanni kusan uku na matsalar tsaro da kasar ta fuskanta.
• Rashin aikin yin matasa
• Talauci
• Gwamnati ta sauke nauyin da ke kanta kafin jama'a su nemi mafita
• Tsarin tsaron da ake bi a Najeriya na da rauni
• Raunin tsarin tattara bayanan sirri ta hanyar intanet
Watakila, za a iya cewa da a ce gwamnati tare da jami'an tsaro sun fahimci ko kuma sun aiwatar da wadannan abubuwa guda biyar da masanan suka zayyana da ba a kai ga yanayin da Najeriya ta samu kanta a ciki a 'yan makonnin nan ba.
Yanzu dai ta bayyana cewa matasa a Najeriyar sun latsa sun ga jini duk da cewa masana na ganin har yanzu kasar mai yawan matasa na da damar sauya al'amura a yanzu da ma nan gaba.
Wannan al'amari dai ya sanya kasashen duniya sanya wa kasar idanu wajen ganin karshen lamarin da irinsa ne ya gurgunta kasashe da dama musamman a nahiyar Afirka da kasashen Larabawa.