Shin Trump zai ƙalubalanci Biden a Kotu?

Trump
A 'yan kwanakin nan, a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri'un zaɓen Amurka, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wasu kalamai marasa tushe inda ya ce an yi "maguɗin" zaɓe kuma ya sha alwashin zuwa kotu. Kalaman nasa sun bar jama'a cikin duhu. Shi da kwamitin yaƙin neman zaɓensa sun kai ƙara kotu a wasu jihohin ƙasar, ciki har da Michigan da Pennyslyvania inda ya buƙaci a dakatar da ƙirga ƙuri'u, amma alƙalan sun yi watsi da buƙatar su. Babban ƙalubale a Pennsylvania shi ne matakin da jihar ta ɗauka na ƙirga ƙuri'un da suka iso ranar zaɓe amma tun tuni an aiko su ne su iso ranar zaɓe sai suka makara iso wa. 'Yan Jam'iyyar Republican na ƙalubalantar wannan mataki. A jihar Wisconsin, kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump ya buƙaci a sake ƙirga ƙuri'un da aka jefa a jihar sakamakon "wasu abubuwa da ba daidai ba da aka gani" a ranar Laraba. Haka ma a hihar Georgia, 'yan Jam'iyyar Republican na jihar da kuma kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump sun gabatar da ƙara a gaban kotu domin dakatar da ƙirga ƙuri'u sinda suke zargin aka matsala wurin ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar gidan waya. Article share tools
Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.