Wani nazari da PREMIUM TIMES ta yi, ya tabbatar da cewa maimakon kasafin kudaden da ake kashe wa jiragen Shugaba Muhammadu Buhari su rika raguwa, sai ga shi tun daga shekarun 2018, 2019, 2020 da 2021, kowace shekara sai yawan na ba na ya fi na bara.
Hakan ya na nufin kenan a cikin shekaru hudu kasafin kudaden da ake ware wa jiragen sun nunka har sun kusa mayawa zuwa kashi 190.
A wannan kasafi na 2021, an ware wa jiragen Buhari naira bilyan 12.5. Amma kuma a kasafin 2017, naira bilyan 4.37 aka ware wa bargar jiragen, wadanda aka fi sani da ‘Presidential Air Fleet’ (PAF).
A shekarar 2017, an kashe wa jiragen naira milyan 399.5 wajen hidimar manyan ayyukan hidimar jiragen. Amma kuma a kasafin 2020, an ware naira bilyan 8,175,622,044 wajen wadannan hidimomin da aka yi da naira milyan 339.5 kacal a 2017.
A kasafin 2018 jiragen Shugaban Kasa sun samu karin kasafin kudi zuwa naira bilyan 7.26. Kasafin 2019 kuma naira bilyan 7.30.
A kasafin 2020 kuma naira bilyan 8.5. Sai kasafin 2021, an ware naira bilyan 12.5.
Ana dirka wa jiragen wadannan makudan kudade ne, duk kuwa da kukan rashin kudin da ake yi, da kuma dimbin bashin da Buhari ke yawan ciwowa a kasashen waje.
A yayin da Buhari a kowane kasafin kudi ya ke gargadin hukumomin gwamnati a rage kashe kudade, a daina fita kasashen waje, shi kuma jiragen sa a duk shekara sai kasafin su ya karu.
Cikin 2015 Buhari ya yi alkawarin zai kwashi wasu jiragen ya kai kasuwa ya sayar, domin a cewar sa, facaka da kudi kawai idan aka ci gaba da rike su. Har gara a sayar da su a samu kudin shiga.
Kamfanin ARIK AIR ne kadai a Najeriya ya fi Buhari tara jiragen zirga-zirga.
Cikin 2015 an rika sukar gwamnatin Jonathan ta tara jirage birjik. Sai ga shi gwamnatin Buhari ta fi ta Jonathan din kashe wa jiragen ahugaban kasa makudan kudade.