Gwamnatin Tarayya ta kafa Kwamitin Farfado da Tattalin Arzikin Kasa, wanda ya tabarbare sakamakon matsi da kuncin da barkewar cutar korona ya haifar a fadin duniya.
Kwamitin mai suna N-CARES, yayin kaddamar da shi dai Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta umarce su da su tabbatar cewa yanayin lokacin da ake ciki bayan cutar korona, bai zama babbar illa ko mummunar barazana ga tattalin arzikin Najeriya ba.
Zainab ta ce kasashen duniya na ci gaba da dandana kuncin da su ka fada, wanda barkewar cutar korona ya yaddasa shi.
Wannan kuncin rayuwa ya fi shafar masu kananan karfi, talakawa, gidajen marasa galihu da manoma wadanda sai sun noma sun girbe sannan za su iya samun abinci.
A kan haka ne gwamnatin tarayya ke kokarin karbo lamunin dala milyan 750 daga Bankin Duniya, a madadin jihohi, domin a yi amfani da kudaden wajen farfado da harkoki, hada-dada da kuma bunkasa tattalin arzikin al’ummar karkara da kananan garuruwan fadin kasar nan.
Kwamitin ya kunshi Ministoci, Manyan Sakatarorin Ma’aikatu. A kwamitin aiwatarwa kuma akwai manyan daraktocin Hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Bashin Dala Milyan 750:
PRWMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Najeriya za ta kara kinkimo sabon bashin dala milyan 750.
A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke kukan rashin cancantar ciwo wani bashin dala milyan 1.2 da Najeriya za ta yi daga Brazil, gwamnatin Najeriya ta sake neman amincewar Majalisar Dattawa ta ciwo wani sabon bashi na dala milyan 750.
Sai dai wadannan kudaden daga Bankin Duniya za a ciwo su, kuma a madadin jihohi za a ciwo basussukan domin bunkasa tattalin arziki a garuruwa da karkara, kuma a inganta tare da tallafa wa wadanda ba su galihu har su rika samun wadataccen abinci.
Ministar Harkokin Kudade Zainab Usman, ta ce shirin na daya daga cikin hanyoyin tayar da komadar dukan da tattalin arziki ya yi wa jama’a sanadiyyar barkewar korona.
Ta yi wannan bayani a wurin kaddamar da Kwamitin Farfado da Tattalin Arziki Bayan Korona.
An kaddamar shirin a Abuja
PREMIUM TIMES ta buga yadda PDP ta nuna damuwa kan wani sabon bashin dala bilyan 1.2 da Najeriya za ta tarkato daga Brazil.
Jam’iyyar PDP ta nuna damuwa dangane da wani sabon bashi na dala bilyan 1.2 da Gwamnatin Tarayya za ta ciwo daga Gwamnatin Brazil.
Cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na PDP, Kola Olagbondiyan ya fitar, ya ce PDP na mamakin irin kunnen-kashin da gwwmnatin APC ke da shi, da ta jajirce sai ta tarkato wannan bashi daga Brazil, duk kuwa da damuwar da ‘yan Najeriya ke ci gaba da nunawa kan yawan bashin da Gwamnatin Buhari ta lafto daga Chana da wasu kasashen duniya.
Gwamnatin Tarayya ta ce ta na neman amincewar Majalisa domin ciwo bashin dala bilyan 1.2 domin a shawo kan wata matsala a bangaren noma.
Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare ce, Zainab Ahmed ta bayyana bukatar amincewar Majalisa kan karbo bashin, a lokacin da ta bayyana a gaban kwamiti ta na kare Kasafin 2021.
Ologbondiyan ya ce wannan bashi zai kara takwarkwashe kwarin guyawun Najeriya, kuma zai zame wa talakawa alakakai, su da al’ummar da ba a ma kai ga haihuwar su ba rukunna a Najeriya.
Ya yi tir da yin amfani da magance matsalar noma don a ciwo bashin, ba tare da yin cikakken bayanin ka’idoji da sharuddan da ke tattare da bashin ba.
Ya yi gargadin cewa ciwo wannan bashi zai maida albarkacin noman Najeriya ya koma aljihun Brazil kacokan, ya kara dankara nauyin bashi a wuyan Najeriya, sannan kuma ya rage karfin zuba jarin kasar nan, tare da haifar da gagarimar matsala a batun wadata kasa baki daya da abinci.
Sannan ya nusar da Majalisar Dattawa cewa “dala bilyan 1.2, daidai da naira bilyan 459 kenan fa. To idan aka hada da wasu naira tiriliyan 5.20 da tuni gwamnatin Buhari ta tsara ciwo bashi domin cike gibin kasafin 2021, to bashin da ake bin Najeriya zai kai naira tiriliyan 36.2 kenan.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta ce bashin da ke kan Najeriya zai iya kai naira tiriliyan 38.68 nan da Disamba 2021.
Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa tulin bashin da ke kan Najeriya zai kai naira tiriliyan 38.68 nan da watan Disamba, 2021.
Zainab ta yi wannan kintacen ne ranar Talata a gaban Kwamitin Bin Biddigin Basussukan Cikin Gida da Waje da ake bin Najeriya, a zauren Majalisar Dattawa.
An gayyaci Zainab ne domin yi wa kwamiti karin haske dangane da tulin bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya da Jihohi 36 har da FCT Abuja.
Hakan kuwa ya biyo bayan yawan damuwar da ake nunawa dangane da yawan wadannan tulin basussukan.
Gwamnatin Buhari dai ta shirya ciwo bashin naira tiriliyan 4.28, domin cike gibin kasafin 2021, wanda Najeriya ba ta da isassun kudaden gudanar da ayyukan kasafin.
Kenan kashi 1/3 na kasafin 2021, duk sai an ciwo bashi sannan za a iya yin ayyukan.
Cikin watan Oktoba ne Buhari ya gabatar da kasafin 2021, na naira tiriliyan 13.08.
To sai dai kuma kintacen kudaden shigar da gwamnatin ta ce za iya tarawa, bai wuce naira tiriliyan 7.886 ba. Saboda haka tilas sai an yi buga-bugar nemo bashin naira tiriliyan 4.28 kenan.
Halin Da Ake Ciki A Yanzu:
Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Kasa, Zainab Ahmed ta ce a yanzu dai bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya, Jihohi 36 da kuma Gundumar FCT Abuja, a jimlace ya kai naira tiriliyan 31.01, daidai da dala biliyan 85 kenan.
Ta ce wannan kididdiga ce fa tun ta ranar 30 Ga Yuni, wadda daga lokacin ba a sake bin diddigi ba.
Dalili kenan ta ce idan aka kai karshen 2021, aka hada da basussukan da Najeriya za ta kara ciwowa, adadin zai kai naira tiriliyan 38.68.
Ayyukan Manyan Titina Za Su Shiga Garari:
Minista Zainab ta shaida wa Kwamitin Kula Da Basussuka cewa akwai matsalar kudi sosai da ta daskare ayyukan manyan titina, kuma a wannan kasafin kudi na 2021 ma a haka abin zai kasance, matukar Najeriya ba ta canja taku ba.
Shawarar da ta bayar ita ce, a daina kwasar ayyukan titina da yawa ana bayarwa kwangila.
Ta ce kamata ya yi a samu shiyya daya a dauki titi daya a bayar da kwangilar sa. Kada a bayar da kwangilar gina wani titin har sai an kammala wancan tukunna.
Ta buga misalin yadda ayyukan titina ke tafiyar hawainiya da cewa, “za a bada aikin naira bilyan 10. Sai an fara ka ga dan kwangila ya zo ya na keman karin kudi. Daga nan idan aka yi buga-buga aka ba shi naira milyan 100, to idan ya je ta kare kuma sai aikin ya tsaya, har sai an sake lalubo wasu kudin an ba shi.”