Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka

Joe biden
Ɗan takarar Jam'iyyar Democrat a zaɓen Amurka Joe Biden ya lashe zaɓen Amurka inda a halin yanzu ya samu kur'iu 273, abokin karawarsa kuma Donald Trump na da 214. A yadda tsarin zaɓen Amurka yake, duk wanda ya fara samun ƙuri'un wakilai na musamman da ke zaɓe har 270, shi ya samu nasara a zaɓen ƙasar. A nasarar da Mista Biden ya samu a jihar Pennsylvania, hakan na nufin ya ci zaɓen Amurka domin kuwa ya samu ƙarin ƙuri'u 20 daga wakilai na musamman masu zaɓe, wanda hakan ya sa ya samu ƙuri'u 273, ya ma wuce 270 ɗin da ake buƙata. Sai dai da alamu Trump ɗin na da niyyar maka Mista Biden ɗin ƙara a kotu biyo bayan wasu zarge-zargen da Trump ɗin ya fara tun a ranar zaɓen inda yake zargin an yi maguɗi, zargin da har yazu bai kawo gamsashiyyar hujja a kai ba. A ƙarƙashin tsarin zaɓen Amurka, masu zaɓe suna zaɓar wakilai na musamman waɗanda ke haɗuwa makonni kaɗan su kaɗa ƙuri'a domin tantance wanda zai zama shugaban ƙasa.
Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.