Kotun Kaduna ta ƙi amincewa da buƙatar dakatar da naɗin sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli
0
11/07/2020 07:43:00 AM
Wata Babbar Kotun Kaduna ta ce ba ta amince da buƙatar da aka shigar gabanta ta neman dakatar da naɗin Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19. A watan Oktoba Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) ya shigar da ƙarar a Babbar Kotun jihar Kaduna da ke Sabon Garin Zariya inda yake ƙalubalantar naɗin Ahmed Nuhu Bamalli a matayin Sarkin Zazzau. Amma a hukuncin da kotun ta yanke ranar Juma'a, alƙalin kotun ya zartar da hukuncin cewa za a iya bikin naɗin sabon Sarkin a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba. Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) na cikin mutanen da suka nemi sarautar ta Zazzau. To amma kotun ta ce za ta gaggauta sauraron ƙarar da aka shigar gabanta. A ƙarar da ya shigar, Iyan Zazzau ya nemi kotu ta tabbatar da shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, kasancewar ya fi samun yawan kuri'un masu zaɓen sabon sarki. A takardun shigar da ƙarar, an yi ƙarar mutane da dama da suka haɗa da gwamnan jihar Kaduna da Antoni Janar na jihar Kaduna da Majalisar Sarakunan jihar Kaduna da Majalisar Masarautar Zazzau da Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu (Wazirin Zazzau) da Alhaji Umaru Muhammad (Faghazin Zazzau). Sauran su ne Alhaji Muhammad Abbas (Makama Karamin Zazzau), da Alhaji Dalhatu Kasimu Imam (Limamin Juma'ar Zazzau) da Alhaji Muhammad Sani Aliyu (Limamin Konan Zazzau) da kuma Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli. Waiwaye A ranar 7 ga watan Oktoba ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da naɗa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19. Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa da ya hau gadon sarauta cikin shekara 100, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a 1920. Sabon sarkin ya fafata da mutane da dama wajen neman sarutar, kuma tuni wasu daga cikinsu irin su Mannir Jafaru (Yariman Zazzau) suka yi mubaya'a a gare shi. A tattaunawa da manema labarai, ya nuna farin cikinsa matuƙa sakamakon Allah ya ƙaddara cewa wannan sarauta ta dawo gidansu kuma a kansa, amma ya ce duk a rayuwarsa, burinsa shi ne mahaifinsa ya yi sarautar Zazzau ba shi ba. Ya kuma ce zai gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci tsakanin sa da sauran gidajen sarautar da suka fafata wajen neman sarautar ba. Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.
Tags