Mutum miliyan 9.8 na fama da yunwa a arewacin Najeriya - MDD

poverty
A baya-bayan nan mutane sun yi ta ɓalle rumbunan gwamnati na ajiyar abinci suna kwashewa, abin da wasu ke ganin yunwa ce ta sa haka Hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan mutum miliyan 10 ne ke fuskantar matsalar yunwa a jihohi 16 da kuma Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Wani rahoton da ta fitar ya nuna jihohi takwas daga ciki na fama da ƙarancin abinci, musamman ma mai gina jiki, yayain da ragowar jihohin kuma ke fama da yunwa. Rahoton ya ce takwas daga cikin jihohin, bayan ƙarancin abinci da suke fuskanta, suna fama da rashin abinci mai gina jiki. Waɗannan jihohin sun hada da Borno da Adamawa da Yobe da Benue da Gombe da Taraba da Katsina da kuma Jigawa. Ɗaya rukunin kuma ya ƙunshi jihohin Kano da Bauchi da Filato da Kaduna da Kebbi da Sokoto da Niger da kuma Abuja, babban birnin tarayya, wadanda rahoton ya ce mazauna jihohin na fama da yunwa. Rahoton ya gano cewa ƙalubalen da ake fuskanta na tabarbarewar tsaro da yawaitar masu gudun-hijira da irin nauyin da suke ɗora wa al'ummomin da ke yankunansu na daga cikin dalilan da ke haddasa matasalar ƙarancin abinci da yunwar. Wace hanya aka bi aka haɗa rahoton? Dr Abubakar Sulaiman, jami'i ne a hukumar ya ce wannan hasashe ya duba daga watan Oktoba zuwa watan Disamban 2020. Ya ce ''ƙwararu ne suka haɗu, waɗanda hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka ba su horo, ma'aikata ne na gwamnati da kuma ma'aikata na ƙungiyoyi masu zaman kansu. Suna tara bayanai na iya adadin mutanen da ke zama a wannan ƙaramar hukuma, za kuma su tara bayanai na iya adadin abincin da ake samarwa ko ake saye a wannan ƙaramar hukumar,'' a cewar jami'in. Dalilin da suka jawo ƙarancin abincin Dr Sulaiman ya ce manyan dalilan da suka haddasa hakan ba su wuce fa,a da ake da tashe-tashen hankula musamman a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma ba. ''Sannan akwai babbar matsalar wadda ita ce annobar Covid-19,'' in ji Dr Sulaiman. Sai dai kuma, duk da irin matsalar tsaron da jihar Zamfara ta fuskanta, rahoton bai sanya ta cikin jihohin da ke fama da matsalar yunwar ba. Amma Dr Abubakar Sulaiman ya ce akwai abubuwan da suka lura da su dangane da hakan. Ya ce ''saboda matsaloli na alƙaluma da a yanzu haka ba su kammalu ba daga jihar Zamfaran, shi ya sa ba za mu iya tantancewa mu fitar da rahoto a kanta ba, irin wanda zai zama rahoto gamsasshe. ''Saboda haka muna ci gaba da tattara bayanai masu gamsarwa kafin mu fitar da trahoto kan abin da ya shafi jihar Zamfara,'' kamar yadda ya ƙara da cewa. Hukumar ta ce akwai buƙatar mahukunta su gaggauta ɗaukar mataki wajen inganta rayuwar mazauna jihohin, saboda lamarin yana da haɗari ga sauran al'umma idan ya munana.
Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.