Rahama Sadau ta ce babu wanda ya kama ta ko ya kai ta kotu

endsars

Fitacciyar ƴar fim ɗin Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta ce ita babu wanda ya kama ta sannan ba wanda ya yanke mata hukuncin ɗauri a gidan yari.


Rahama ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita a ranar Talata da yamma, bayan da bayanai ke ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta cewa an kama ta an kai ta Kotun Shari'ar Musulunci kan zargin ta da hannu a ɓatancin da aka yi wa Manzon Allah.
Ta ce: ''Ban san daga ina labarin nan ya samo asali ba. Don haka ina kira ga mutane da su daina yaɗa labaran ƙarya marasa makama...''
A makon da ya gabata ne Rahamar ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Tuwita da ke nuna bayanta a buɗe, inda mutane suka yi mata rubdugu da tofin Allah tsine.
Duk da wasu na caccakar jarumar game da hotunan da ta wallafa, wasu kuma kare ta suka yi.
Mafi yawan wadanda suka fito daga yankin kudancin Najeriya na yabon hotunan, yayin da waɗanda suka fito daga arewaci ke suka, inda har wani ya yi kalaman ɓatanci kan Annabi Muhammadu a ƙasan hotunan, lamarin da ya ɗauki wani sabon salo.
Daga baya jarumar ta fito ta bayar da haƙuri kan abin da masu ɓatancin suka yi, ta kuma goge hotunan gaba ɗaya.
Sai dai duk da haka zancen bai mutu ba don kuwa a ƙarshen makon da ya gabata rundunar 'yan sandan Najeriya ta bai wa kwamishinan 'yan sandan Jihar Kaduna umarnin ɗaukar mataki kan Rahama, bayan da wani mutum mai suna Lawal Gusau ya kai ƙararta ga 'yan sandan kan hotuna da ta wallafa ɗin da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

'Ba wanda ya kama ni'

A cikin jerin saƙonnin da ta wallafa ɗin jarumar ta ci gaba da cewa ta samu saƙonni da dama kan cewa an kama ta tare da yanke mata hukuncin zaman gidan yari a ranar Talata.
''Ni ban samu saƙon gayyata daga ƴan sanda ko sammacin kotu ba. Ina sake jaddada wa masu yi min fatan alheri cewa ina nan lafiya lau kuma babu wata tuhumar shari'a da na samu."
''Ga masu son mayar da wannan batu wani abu daban da zai jawo rashin zaman lafiya, na roƙe ku bar shi haka..!!!
''Yanzu lokaci ne mai tsanani a gare ni. Ba lokaci ne na yaɗa labaran ƙarya ba. Ina godiya sosai ga waɗanda suka tuntuɓe ni," in ji ta.
Ta ina zancen ya samo asali?
Da safiyar ranar Talata ne labari ya fara yaɗuwa a shafukan sada zumunta cewa za a gurfanar da jarumar a gaban Kotun Shari'ar Musulunci don tuhumarta da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad.
Sai dai har yanzu babu tabbacin daga ina 

zancen ya samo asali.

An ƙirƙiri maudu'ai da suka haɗa da #Rahama Sadau da #Qur'an da #Islam da #Fake News inda aka yi amfani da su sau dubbai.
Muhawarar ta ranar Talata ma dai ta karkata ne tsakanin Musulmai ƴan arewacin ƙasar da Kiristoci daga kudanci masu kare ta.
Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.