Wani lauya ya kai CBN ƙara kotu domin a cire haruffan Larabci daga jikin naira

endsars

Wata kotu a birnin Lagos da ke Najeriya za ta saurari karar da wani lauya ya shigar a gabanta inda yake so a tilasta wa babban bankin kasar CBN ya cire harufan Larabci daga takardun kudin kasar.

A ranar Talata kotun za ta saurari karar.
Kazalika Malcolm Omirhobo yana so kotu ta tilasta wa rundunar sojin kasar ta cire harufan Larabci da ke jikin tambarinta yana mai cewa yin hakan tamkar Musuluntar da Najeriya ne sabanin kundin tsarin mulkin kasar da ya nuna cewa kasar ba ta jingina da wani addini ba.
Lauyan yana so a maye gurbin harufan Larabci da na Turancin Ingilishi ko kuma daya daga cikin manyan harsunan kasar - Hausa, Yoruba ko Igbo.

Sai dai babban bankin kasar ya musanta cewa harufan na Larabci wata alama ce ta Musulunci.
Mutane da dama a kasar, musamman wadanda ke zaune a arewacinta, suna magana da harshen Larabci. Ko da yake Turancin Ingilishi ne harshen da ake magana da shi a hukumance.
Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.